By Ishaq Dabai
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA ta yi kira da a dauki kwararan matakai don dakile afkuwar abubuwan da ke faruwa na dabi’a da mutane ke haifar da bala’i.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Hajiya Zainab Sa’idu, Shugabar Ofishin Ayyuka na NEMA, don tunawa da ranar Rage afkuwar bala’i na shekarar 2021 a Minna, ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya bayyana cewa taken ranar ta shekarar 2021 shine: “Haɗin kai na ƙasashen duniya don ƙasashe masu tasowa don rage haɗarin bala’i da asarar bala’i.”
Ya kasance kashin manufa bakwai na duniya na tsarin Sendai don rage haɗarin bala’i da aka kafa a cikin shekarar 2016.
Zainab tace jigon ya yi daidai da hangen nesar hukumar NEMA na neman ƙirƙirar al’ummomin da bala’in ya shafa a duk faɗin ƙasar.dan rage haɗarin bala’i zuwa mafi ƙarancin ƙima.Ta shawarci gwamnatocin Neja da Kwara dana al’umma, shugabannin gargajiya da na addini dasu himmatu wajen kawo sauyi a jihohin su, da nufin dakile faruwar bala’o’i da dama wadanda za a iya hana su afkuwa.
Jami’ar NEMA ta kara da cewa, “Wannan ba wai kawai zai ceci rayuka ba har ma da adana albarkatun jama’a, rage barna da gujewa asarar daka iya faruwa daga afkuwar bala’i.”Gwamnatin Tarayya ta ba da jerin shirye -shirye ta a jihohin Neja da Kwara don tallafawa wadanda bala’i ya rutsa da su, don yin hidima a matsayin bada taimako.”
Kazalika Zainab ta bukaci mutanen jihohin biyun dasu guji ayyukan da ka iya jefa rayuwarsu cikin hadari, ciki har da kauracewa zubar da shara ba bisa ka’ida ba a kan hanyoyin ruwa, da yin gini a filayen da ambaliyar ruwa take bi