A ranar Lahadi ne Newcastle ta sanar da daukar dan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes daga Lyon kan kwantiragin shekaru hudu da rabi kan kudin da ba a bayyana ba, Amma an ruwaito cewa kudin, ya kai kusan fam miliyan 40 (dala miliyan 54).
Guimaraes, mai shekara 24, shi ne Dan wasa na uku da Eddie Howe ya dauka a kasuwar musayar ‘yan wasa, bayan zuwan dan wasan Ingila Kieran Trippier da Chris Wood na New Zealand.
Howe ya ce “Bruno kwararre ne mai ban sha’awa kuma ya kasance daya daga cikin manyan abubuwan da muka sa a gaba, don haka na yi farin cikin tabbatar da shi,” in ji Howe.
“ Ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yan wasa a Faransa kuma cikakken dan kasar Brazil ne. ”
Rahotanni sun nuna cewa farashin dan wasan ya kai Yuro miliyan 40 (£33m), tare da karin Yuro miliyan 8 Idan yayi katabus.
An kuma ruwaito cewa Newcastle ta kulla yarjejeniya da Brighton kan dan wasan baya Dan Burn, wanda aka yi imanin ya kai kusan fam miliyan 13 (€15.6m).
Kungiyar ta Magpies dai na murza karfin tattalin arzikinta nea karkashin sabon mamallakar kungiyar da Saudiyya ke jagoranta a wani yunkuri na kaucewa faduwa daga gasar Premier.
Za su kara da abokan hamayyarta Everton a wasansu na gaba a gasar Premier, ranar 8 ga Fabrairu.
Mai horas da kungiyar Howe ya ce a ranar Juma’a kungiyar za ta ci gaba da Neman Yan wasa a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu.
“Muna aiki tukuru don inganta kungiyar,” in ji shi. “Babban burinmu shine mu baiwa kungiyar dama mafi kyawu ta ci gaba da zama a gasar.”