Orji Kalu ya bayyana haka a lokacin da yake wata zantawa da Kamfanin Dillancin Labaru na Kasa wato-NAN.
Idan dai ba’a manta ba majiyar jaridar Dimokuradiyya a ranar 15 ga watan Juli ta ruwaito cewa, Sanatoci 52 ne suka kada kuri’ar gudanar da zabe ta hanyar yanar gizo a Babban zabe mai zuwa na Shekarar 2023, a yayinda Sanatoci 28 suka kada kuri’ar rashin amincewa akan gudanar da hakan, inda Sanatoci 28 basu samu zaman Majalisar daya gudana.
“Kamar Abia ta Arewa inda na futo, babu layukan sadarwa a wasu wuraren, akwai dai kashi 43, to taya zamu gudanar da zabe akan hakan, nayi imani akan tura sakamako ta hanyar yanar gizo, amma ina so inyi kira ga Hukumar NCC da tayi gaggawar kawo fasahoh,i domin tabbatar dacewa akwai layukan sadarwa a ko’ina, nayi imani akan wannan hanyar domin akwai gaskiya acikin ta.
“duk abunda zanyi sai na tabbatar zai amfani dukknanin yan Nigeria,” inji Kalu.