Yadda Sanata Uba Sani Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, ya gina katafariyar cibiyar koyar da sana’o’i a Sabon garin Nasarawa Tirkania dake karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Wanda yanzu Haka an dai mika aikin watanni biya 2 da Suka wuce, inda yanzu haka cibiyar na hannun Jagorancin karamar hukumar ta Chikun, kuma an Samar da cibiyar ne domin koyar da Mata da matasa sana’o’i daban-daban domin dogara da Kan su.
Idan baku manta ba Sanata Uba Sani shine Shugaban kwamitin inshora bankuna da Sauran harkokin kudi a majalissar Dokokin kasar nan, ku.a Sanatan shine Jagoran wajen Bayarda Rance ga Manoma daga bankin CBN, Wanda bankin NIRSAL ke bayar wa ga manoma Yan Nageriya domin su amfana da tsarin.
Sanata Uba Sani shine Sanata mafi aiki a majalisar ta Tara, kamar yadda hukamar Bincike ta Midterm Dake majalisar ta tabbatar a satin daya gabata.