Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a ya ce Najeriya za ta hada gwiwa da Kasar Turkiyya wajen tunkarar kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu.
A cewar fadar shugaban kasar, hakan ci gaba da kokarin tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya.
Da yake magana a taron kasashen biyu Recep Tayyip Erdogan, takwaransa na Turkiyya jim kadan gabanin fara taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na 3 a birnin Istanbul, shugaba Buhari ya bayyana cewa, Turkiyya ta samu kwarewa sosai wajen tunkarar kalubalen tsaro iri daban-daban kuma Najeriya za ta yi aiki tukuru don samun wannan kwarewa.
Shugaba Buhari ya ce, “Turkiyya na da kwarewa a aikace wajen tunkarar kalubale a tsawon shekaru kuma Najeriya za ta ci gajiyar hakan.”
Da yake ba da tabbacin alakar da ke tsakanin jihohin biyu za ta ci gaba da bunkasa domin samun moriyar juna, shugaba Buhari ya ce ya ji dadin tallafin da Turkiyya ke yi a fannin tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
“Ina so in nuna jin dadina ga gayyatar da aka yi min na musamman na wannan taro da kuma nuna farin cikina da taimakon da kuke yi na tunkarar kalubalen da ke gabanmu.
‘’Ina jiran rahoton jami’ai da ministoci yayin da suke ganawa da takwarorinsu. Ina ba ku tabbacin cewa zan amince da duk shawarwarin da suka bayar,” Shugaba Buhari ya tabbatar wa Erdogan.
Tun da farko shugaban na Turkiyya ya ce ya yi farin cikin tarbar shugaba Buhari jim kadan bayan ya kai ziyarar aiki Najeriya.
“Turkiyya ta fahimci kalubalen da Najeriya ke fuskanta da kuma bukatunta, kuma a shirye muke mu taimaka muku wajen biyan wadannan bukatun musamman a fannin tsaro.
“Na yi farin ciki cewa Najeriya na kara yin hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin tsaro da kiwon lafiya, kuma a shirye muke mu ba ku hadin kai kan wadannan fannoni da ma sauran su,” in ji Shugaba Erdogan.
Kasar Turkiyya wadda ke kara samun karbuwa a duniya a matsayin kasa mai karfin soji kuma ta samu nasarori a kasashen Iraki da Siriya da Libiya da kuma Azabaijan a baya-bayan nan, ta ce ta yi maraba da matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na sayen jiragen ruwa daga tashar jirgin ruwansu, inda ta ce ana ci gaba da tattaunawa kan yadda za a karfafa karfin Hukumar Ma’aikatun Tsaro (DICON) da ke Kaduna bisa yarjejeniyar da aka kulla a ziyarar da Shugaba Erdogan ya kai na karshe.
Comments 1