Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a ranar Laraba ya ce Najeriya ta samu a cikin shekaru 24 abin da Amurka bata samu ba cikin shekaru 185.
A jawabinsa yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a zaman hadin guiwar ‘yan majalisar a zauren majalisar a ranar Laraba, ya ce, tsoffin ‘yan majalisar dattawa sun mamaye manyan mukamai a bangaren zartaswa wanda hakan yasa dole a hada hannu don samar da kyakkyawar alaka.
Karanta nanZa A Cigaba Daukar Jami’an ‘Yan Sanda 30,000 Aiki Duk Shekara-Tinubu
Akpabio ya ce tare da tsaffin ‘yan majalisar da ke gudanar da zartaswa, dangantaka mai kyau tsakanin hannayen biyu ba kawai zai zama dole ba, amma za su ci gaba da tafiya kafada da juna.
Mai girma shugaban kasa, Amurka ta fara mulkin dimokuradiyya kusan shekaru 247,sai dai lokacin da aka yi bikin cika shekaru 185 da samun nasarar samar da tsaffin Sanatoci biyu John F Kennedy da Lyndon B Johnson a matsayin shugaban kasa da mataimakinsa.
Amma a cikin shekaru 24 na dimokuradiyyarmu, mun cimma abin da Amurka ta dauki shekaru 185 don cimmawa,” in ji shi.
Ba wai kawai muna da tsofaffin Sanatoci guda biyu da ke aiki a matsayin Shugaban kasa da Mataimakin Shugaban kasarmu ba; Haka nan muna da sauran tsofaffin daliban wannan Majalisar da ke rike da amanar jama’a.
A wani labarin kumaMajalisar Dokokin Bauchi ta Zabi Sabon Shugaba
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Rt Hon. Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai, da wasu Sanatoci a majalisar zartarwa.
Shugaban kasa, masu girma da daukaka, ci gaba da kulla kyakkyawar alaka da bangaren zartarwa abu ne da doka ta tanada, amma yanzu, ganin cewa tsofaffin yaranmu ne ke tafiyar da zartaswa, kyakkyawar alaka da bangaren zartaswa ya zama tilas.