Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta mayar da mai shari’a Babajide Aladejana na babbar kotun jihar Ekiti aiki bayan shafe shekaru 16 da dakatar da shi,Vanguard ta rawaito.
An dakatar da Aladejana daga aiki a shekarar 2006 tare da tsohon babban alkalin jihar, Mai shari’a Kayode Bamisile, a karkashin gwamnatin tsohon alkalin alkalan Najeriya, Mai shari’a Alfa Belgore.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Ya Isa Borno Domin Ƙaddamar Da Wasu Ayyuka
An dakatar da ‘yan biyun ne bisa zarginsu da taka rawa a rikicin siyasar da ya kai ga tsige tsohon Gwamnan Jihar, Ayodele Fayose a ranar 16 ga watan Oktobar shekarar 2006, bisa zargin badakalar Naira biliyan 1.4 na kiwon kaji, cin zarafi da gudanar da wani aiki ba bisa ka’ida ba asusun kasashen waje.
Sai dai Aladejana ya koma bakin aikinsa a hukumance ranar Talata, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Dage dakatarwar da aka yi masa ya biyo bayan bitar hukumar NJC.
Daga nan sai aka ba shi babbar kotu mai lamba biyu inda zai saurari kara da kuma gudanar da wasu ayyuka na shari’a.
A wani labarin kuma, Yadda Atiku Ya Tarwatsa Jam’iyyar PDP – Kiyamo
Kakakin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC,PCC, Festus Keyamo, ya bayyana yadda jam’iyyar PDP ta lalata kanta da kanta.
Keyamo ya ce rashin kishin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya taimaka wajen ruguza jam’iyyar adawar.