Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta bukaci babban bankin Kasa CBN ya kara wa’adi daga ranar 31 ga watan Janairu domin kawar da tsofaffin takardun kudi da ake amfanj da su a kasar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Mista Ayuba Wabba, shugaban kungiyar ta NLC, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Abuja kan nasarorin da ya samu da kalubalen da ya fuskanta a matsayinsa na shugaban majalisar kungiuar na tsawon shekaru takwas.
Kamfanin dillancin labaran Kasar nan (NAN) ya rawaito cewa Wabba, wanda aka zaba a matsayin shugaba na kasa a shekarar 2015, ya yi wa’adi biyu ne.
KU KARANTA KUMA Kungiyar Kwadago NLC Ta Bukaci Buhari Ya Kara Yawan Albashi
Wabba ya ce umarnin da majalisar dattawa ta bayar na neman a kara wa’adin abu ne da ya dace.
Ya ce hakan ya biyo bayan yadda akasarin ‘yan Najeriya da ke zaune a lungu da sako na kasar da babu bankuna har yanzu ba su samu damar shigar da sabon kudin Nairar ba.
A cewarsa, a matsayinmu na NLC, “mun yi kokarin mayar da martani a hukumance ta hanyar rubutawa gwamnan CBN wasika. Mun kuma rubuta wa shugaban kasa cewa, wannan sabuwar manufar ta sauya Nairar tamu tana bukatar a sake duba ta.
“A bayyane yake cewa ko a cikin manyan biranen, bankuna suna ba da tsofaffin takardun kudi kuma wannan ba daidai ba ne. Na tuna, na je kusan bankuna 10 kuma babu wanda ke rarraba sabbin kudin.
“A gaskiya, yawancin bankunan yanzu, idan kun yi sa’a, za su ba da takardun kuɗi kaɗan ne kawai kuma za ku iya duba hakan.
“Don haka ba a samu sabbin kudin ba kuma ba sa yaduwa kuma ana watsi da tsoffin.
“Ko a cikin birane, inda muke da bankuna, bankunan ba sa rarrabawa.
“Idan ka je yankunan karkara ka ga yanayin rudani na yadda mutane suka zo da kudadensu suna canjawa, ya zama matsala,” inji shi.
Ya kara da cewa babu wata manufa da za a yi nufin a zahiri ta cutar da mutane kamar abin da ke faruwa a yanzu.
Jaridar Solacebace ta rawaito cewa Don haka shugaban NLC ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba lamarin a tsanake kafin a kai ga shiha cikin wani babban rikici a kasar nan.
A Wani Labarin Kuma Tinubu Ya Zargi PDP Da Yin Zagon Kasa Ga Samar Da Man Fetur, Da Bata Sunan FG
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya zargi jam’iyyar PDP da yin zagon kasa ga samar da man fetur a kasar nan domin bata wa gwamnatin tarayya a siyasance.
Da yake jawabi a garin Markurdi, babban birnin jihar Benuwe, ga dimbin magoya bayan jam’iyyar da suka halarci gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Tinubu, ya bayyana cewa, a lokacin da gwamnatin PDP ke kan karagar mulki, ta ba magoya bayansu lasisin sayar da man fetur, wadanda a yanzu haka suke tara man fetur don samar da dogayen layuka a fadin kasar da kuma sanya ‘yan Najeriya cikin wahala, inda ya kara da cewa jam’iyyar babban mai kalubalantar sa Atiku Abubakar jam’iyyar Raya Talauci ce.