NMA ta buƙaci Adalci ga ƴan uwan Majinyacin da suka Jikkata Likita
Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jahar Bauchi tayi Allah wadai da harin da aka kaiwa wani mamban ta da makami, wanda shine Babban Likitan Babban Asibitin Misau Dr. Mohammed Sani, daga wani kawu na matar data haihu a Asibitin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahara sun bankawa marasa lafiya wuta da ran su a DR Congo
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba, Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya reshen Jahar Bauchi, Dr. Adamu Sambo, yace ya farmake shi da Gatari, a wani yunkuri na hallaka akan yanda aka kula da ɗiyar ƴar uwar sa.
Yace anyi saurin kai Matar Babban Asibitin Misau akan haihuwar ta, amma sai ta samu wasu cututtuka da sai anyi mata tiyata.
“Abinda ya faru shine wani Marar lafiya yazo Asibitin su, ina tunanin kodai turo ta akayi daga wani Asibiti, ko kuma sun zo akan raɗin kansu, akan haihuwa. Wannan shine karo na farko da Matar zata haihu, amma sai suka ƙi bayyana haka.
“A lokacin da aka bincike ta sai aka gano bazata iya haihuwa ba, to sai suka yi amfani da wata hanya domin ganin ta haihu.
“Bayan ta haihu sai ta fitar da jini, amma sun kai ta wajen tiyata domin ganin an yi mata aiki.