NUT ta yaba ma Gwamna Oborevwori akan samar da ɗinbin aikin yi a Jihar Delta
Kungiyar malamai ta Najeriya NUT reshen jihar Delta ta yabawa gwamna Sheriff Oborevwori
bisa ɓullo da sabbin ayyuka sama da 2000 a faɗin Makarantun Firamaren Jihar.
Shugaban Ƙungiyar NUT reshen Jihar Comrade Titus Okotie ya bayyana ƙoƙarin Gwamnan a matsayin tallafi da zai bunƙasa tattalin arzikin ɗinbin Ɗaliban da suka kammala karatun digiri a Jihar da kuma nuna wata alama da ke bayyana ƙoƙarin Gwamnan na ganin ya inganta bangaren ilimin Jihar.
Okotie ya ce “Batun ƙarancin Malamai musamman a Makarantun Firamare Abu ne da ya Daɗe yana ci ma al’ummar Jihar tuwo a ƙwarya, wanda Gwamnan da kanshi yayi tsokaci akai a lokacin yaƙin neman zaɓe, inda yayi alkawarin fuskantar matsalar gadan-gadan da zaran ya samu nasara.
Kungiyar dai ta gana da Gwamnan a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, inda matsalar ƙarancin Malaman na daga cikin batutuwan da suka tattauna da shi domin a haɓaka harkar koyo da koyarwa a Jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Nine Shugaban Kasar Najeriya Da Bazan Yaki Kasar Nijar Ba-Peter Obi
A yayin zantawar, kungiyar ta gabatar mashi da shawarar cewa zai fi chanchanta idan ya haɗa hannu da ita musamman wajen kafa kwamitin da zai jagoranci lalubo bakin zaren matsalar da kuma yadda za a magance ta.
“Da wannan ne bayan ya hau mulki, sai ya kafa kwamitin haɗin gwiwa, tare da bada dukkanin goyon bayan da ake buƙata inda daga bisani ya amince da ɗaukar ƙarin malamai 2000 domin inganta ilimi a Jihar.
A cewar Shugaban Kungiyar, duk da cewa adadin Malaman da aka amince za a ɗauka ba zai magance dukkanin matsalar ƙarancin Malaman ba, amma ya zama wajibi a yaba ma Gwamnan da irin wannan namijin ƙoƙari da yayi.
Okotie ya bayyana cewa a shekarar 2005 Jihar tana da Malamai kimanin 27,000 wanda ya ce sun ragu zuwa 17,000 a shekarar 2015, sannan kuma yace a wannan shekarar da muke ciki, sun ƙara raguwa zuwa 10,000 na ainafin malaman din-din-din.
Ya ce Gwamnan ya bayyana wannan ne a matsayin mafari, kuma akwai wasu da yawa da za a ƙara ɗauka nan gaba.
A wani labarin kuma:Har Yanzu Malamai 300 Ba Su Karbi Albashin Su Ba a Kaduna – NUT