Kociyan tawagar kwallon ƙafa ta ƙasar Italiya Roberto Mancini ya ajiye aikinsa na horar da kasar a Lahadinnan.
Hukumar kwallon kafa ta Kasar FIGC ce ta sanar da hakan a yau cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce Mancini ya ajiye horar da zakarun kasashen na nahiyar turai din ne bisa raɗin kansa.
FIGC ta ce ta wannan sanarwa ta shammaceta matuƙa, toh amma ta ce ba za ta yi jinkiri ba wajen sanar da sabon mai horar da tawagar kasancewar ana ci gaba da fafutukar neman gurbin shiga gasar kasashen nahiyar turai ta 2024.
“Saboda muhimmancin wasan da za mu buga da kasar Macedonia da kuma Ukraine, FGIC za ta sanar da sabon kocinta cikin yan kwanaki masu zuwa”
An naɗa Mancini a matsayin kocin Italiya ne a watan Yunin 2018 bayan da kasar karkashin Gian Piero Ventura ta gaza samun tikitin gasar cin kofin duniya da ta gabata a kasar Qatar.
Mancini wanda dan asalin ƙasar ta Italiya ne ya samu damar lashe gasar Euro ta 2021 toh sai dai ya gaza ka ga kasar zuwa cin kofin duniya ta Qatar.
Kuma wannan sanarwa ta zo mutane da mamaki ganin cewa bai nuna wata alama ta yin murabus ba.
Toh sai dai a farkon wannan wata ne aka bashi horar da tawagar yan lasa da shekara 21 da kuma yan kasa da shekara 20.
Yanzu haka dai tuni aka fara hasashen wanda zai maye gurbinsa inda jaridu da dama suka fara bayyana sunan kocin kungiyar Napoli bayan kawo karshen shekara 33 sa kungiyar ta yi ba tare da lashe gasar Serie A ba.