Kungiyar Dattawan Afirka ta Yamma (WAEF) ta tura tawagar tantancewa zuwa Saliyo, gabanin babban zaben kasar da aka shirya yi a watan Yunin 2023,Tribune Online ta rawaito.
Tawagar WAEF wadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke jagoranta kuma tana da tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan da tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Gambia, Fatoumata Tambajang a matsayin mambobi.
KARANTA WANNAN LABARIN: FEC Ta Amince Da Miliyan N495m Don Sanya Na’urorin Daukar Hoto A Tashoshin Jiragen Kasa
Za su yi mu’amala da manyan shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a Saliyo a matsayin hanyar zurfafa kwarin gwiwa da amincewar ‘yan kasar kan tsarin zaben.
A ranar Laraba, 12 ga watan Afrilu, 2023 ne aka fara aikin na kwanaki biyu domin nuna goyon baya ga babban zaben kasa mai cike da lumana.
Wakilan tawagogin za su yi shawarwari da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar kasar, da suka hada da kungiyoyin farar hula da jami’an diflomasiyya da hukumomin zabe a wani yunkuri na tabbatar da shirin gudanar da zabe na gaskiya da adalci.
Wata sanarwa da gidauniyar Goodluck Jonathan mai masaukin baki WAEF ta fitar, ta jaddada cewa tawagar ta Saliyo ta yi daidai da manufar dandalin na inganta diflomasiyya na rigakafi a matsayin hanyar rage tashe-tashen hankula masu nasaba da zabe a Afirka.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa an kafa WAEF ne a cikin shekarar 2020 don inganta zaman lafiya, dimokuradiyya da shugabanci na gari, kuma ta gudanar da ayyukan diflomasiyya na rigakafi a kasashe da dama ciki har da Gambia da Najeriya.
Bayan ayyukanta a Saliyo, WAEF na shirin gudanar da irin wannan aiki a Laberiya, kasashe biyu da ke gudanar da babban zabe a shekarar 2023.
Jim kadan bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, WAEF ta tura tawagar tsaffin shugabannin kasar domin tattaunawa da wasu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki, inda ta kai musu sakon zaman lafiya domin tabbatar da an samu hakan ba wani tashin hankali bayan zabe a kasar.
Zaben da za a yi a Saliyo a shekarar 2023 shi ne zaben dimokuradiyya na shida a kasar kuma shi ne na biyar tun bayan kawo karshen yakin basasa a shekara ta 2002.
A wani labarin kuma,PDP Ta Musanta Dakatar Da Dino Melaye
Jam’iyyar PDP reshen jihar Kogi ta musanta rahotannin da kafafen yada labarai suka yada cewa ta dakatar da tsohon dan majalisa Dino Melaye, kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Jam’iyyar PDP a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Farouk Yahaya, sakataren jam’iyyar na jihar ta bayyana cewa babu wani lokaci da ta yi tunanin dakatar da dan takararta na gwamna.