Wani ginin bene mai hawa 7 wanda ake aikin ginawa a Banana Island da kd jihar Legas ya rufta, inda ya ritsa da ma’aikata da dama.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an aike da jami’an bayar da agajin gaggawa zuwa wajen da ginin ya rushe.
KU KARANTA KUMA: Kwamacala: An Maka Wani Mutum A Kotu Bisa Zarginsa Da Auren Mata Biyar
Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) na jihar Legas ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata ƴar gajeruwar sanarwa da ya fitar.
Da yake bayar da ƙarin bayani kan rushewar benen, mataimakin darektan ministirin tsara birane ta jihar, Mukaila Sanusi, ya bayyana cewa wani bene mai hawa bakwai wanda ba a amince da shi ba ya rushe.
A kalamansa:
“Ana duba lafiyar mutane ƴan ƙalilan da suka samu raunika. Ba a samu asarae rai ba. Lamarin ya auku ne lokacin da ake zuba kankare.”
“Kwamishinan tsara birane na jihar, Engr. Tayo Bamgbose-Martins ya ziyarci wajen lamarin na aukuw domin ganewa idon sa halin da ake ciki da kuma fara gudanar da bincike.”
“Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankulan su sannan su jira ƙarin bayani daga bakin ministirin.”
Wannna lamarin dai shine na baya-bayan da gini ya ke ruftawa a jihar Legas.
Mutane 15 Sun Kone Kurmus A Wani Hatsarin Mota
A wani labarin na daban kuma, wani mummunan haɗarin mota ya janyo asarar rayuka da dama.
Akalla mutane 15 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a jihar Enugu ranar Asabar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Bisi Kazeem ya sanyawa hannu a ranar Lahadi, ya ce hatsarin titin ya faru ne sakamakon wuce gona da iri da kuma keta haddin hanya.