Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain dake ƙasar Faransa ta kafa wani mummunan tarihi a gasar French League 1 ta ƙasar Faransa a bayan da tayi rashin nasara har gida a hannun abokona hamayyarsu wato Marselle daci 1 da nema.
Paris Saint Germain dai sune zakarun gasar ajin League One ta ƙasar Faransa amma kuma a yanzu sun buga wasanni guda 2 a sabuwar kakar wasan da aka fara wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021.
A makon farko dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa Lens ta sami nasara a kan P.S.G daci 1 mai ban haushi inda kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Olympique Marseille ta sake wanketa a daren jiya daci 1 da nema, inda a yanzu P.S.G bata da maki.
A mako mai zuwa P.S.G zata fafata wasan mako na 3 da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Metz, saidai mai horas da Paris Saint Germain ya fara gamuwa da suka ganin yadda ya fara yin rashin nasara tun a farkon kakar wasan da aka fara ta bana.
Ana ganin har yanzu akwai burbuɗin zafin rashin nasarar da P.S.G ɗin tayi a wasan ƙarshe na gasar zakarun nahiyar turai a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich daci 1 da nema.