Gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanonin layukan wata umurnin dakatar da kwasar naira 20 daga asusun masu duba lambar shaidar zama dan kasa (NIN). Inda suka ce umurnin ya fara nan take.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami ne ya bada umurnin a ranar Juma’a a wata sanarwa da ya fitar.
Ministan ya ce yin hakan zai bai wa kowa damar duba lambar cikin sauki.