PDP ta rusa kwamitin zartarwa na jihar Katsina
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP, ya amince da rusa kwamitin zartaswar jam’iyyar na jihar Katsina ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a Abuja ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zaɓen Najeriya: Burtaniya za ta haramtawa masu siyan kuri’u da masu adawa da dimokuradiyya biza
Ologunagba ya bayyana cewa NWC ta dauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi kan al’amuran da suka shafi jam’iyyar reshen jihar Katsina.
Ya ce matakin na kwamitin na ƙasa ya ɗauki matakin duba da sashe na 29 (2) (b) da 31 (2) (e) na kundin tsarin mulkin PDP (kamar yadda aka gyara a shekarar 2017).
Ologunagba ya bukaci daukacin shugabanni, masu ruwa da tsaki da jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar da su kasance da hadin kai tare da mai da hankali kan aikin da ke gabansu.
A wani labarin kuma:Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan azumin Ramadan
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, Mohammed Abubakar, ya sanar da fara azumin watan Ramadan.
Abubakar ya ce an ga jinjirin watan azumin Ramadan.