Ramadan: Buhari ya aika wani saƙo ga musulmi yayin da za’a fara azumi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon gaisuwa da fatan alheri ga al’ummar musulmi yayin da za’a fara azumin kwanaki 30 na azumin watan Ramadan.
Buhari ya bukaci Musulmai da su yi amfani da lokaci “don tsara kyawawan dabi’u na Musulunci ta hanyar dabi’a.”
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan azumin Ramadan
A cikin sakon fatan alheri na ganin watan Ramadan mai alfarma, Buhari ya ce “mu yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da mafi kyawun koyarwar addinin Musulunci, kamar kyautatawa da son bil’adama.”
A cewar shugaban, “Wannan wani lokaci ne na zurfafa tunani da kuma tsoron Allah da kuma nisantar duk wani sharri da ke cutar da bil’adama.
“Ramadan ana kauracewa abinci da abin sha tun daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana, wanda masu hannu da shuni suke raba abubuwan alheri tare da karfafa dankon zumunci tsakanin mawadata da marasa ƙarfi”.
Buhari ya bayyana cewa, “Yayin da muka fara azumin kwanaki 30 din nan, kada mu manta cewa Ramadan ba wai kawai kaurace wa ci da sha ba ne, a’a abin tunatarwa ne a kan nisantar duk wani abu na sharri da keta haddi da ke cutar da bil’adama.
“Ina sane da ayyukan ‘yan kasuwa da ke kara farashin kayayyakinsu ta hanyar roba, ciki har da abinci a farkon kowane wata na Ramadan. Irin wannan cin gajiyar ya saba wa ruhin Ramadan da ruhin Musulunci”.
Buhari ya kara da cewa, “a yayin da muke gudanar da wannan muhimmin biki a rayuwar musulmi, mu rika raba abinci da abin sha ga marasa galihu, domin ta hanyar raba ni’imominmu da sauran mutane, Allah zai rubanya mana ladan ayyukan alheri.
A wani labarin kuma:PDP ta rusa kwamitin zartarwa na jihar Katsina
Kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP, ya amince da rusa kwamitin zartaswar jam’iyyar na jihar Katsina ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya fitar a Abuja ranar Laraba.