Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi, inda shugaban jam’iyyar na jihar Akwa Ibom, Mr Ekpenyong ya mutu ne ranar Litinin a Uyo, kamar yada wani jami’in gwamnatin Akwa Ibom wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatarwa jaridar Premium Times.
Jami’in ya ce cutar korona ce ta kashe Mr Ekpenyong.
Kafin zaɓensa a matsayin shugaban jam’iyyar reshen Jihar a bara, shi ne kwamishinan kananan hukumomi da harkokin cikin gida na jihar.
Makusanci ne na ƙut da ƙut ga Gwamna Udom Emmanuel.