A jiya Lahadi Jami’iyar adawa ta PDP reshen jihar Adamawa, ta zargi Sanata Grace Bent da yi wa jam’iyar zagon kasa, biyo bayan komawar ta jam’iyar APC Mai mulki
Sakataran tsare-tsaren jam’iyar Hamza Madagalli ne, ya bayyana wa manema Labarai hakan, inda ya ce, Tsohowar Sanatan ta ci dun-duniyar jam’iyar PDP na tsawon Shekaru biyu da su ka gabata, bayan ta yi rashin nasara a hannun Sanata Ninos Dauda Yero, lokacin zaben fidda gwani da ya gudana a yankin Kudancin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Eedris Abdulkareem zai saki sabuwar wakar Jagajaga, Ya sake caccakan Obasanjo
Madagli ya ce, an dauki tsawon lokaci Bent ba ta da wani tasiri a harkan siyasar jihar, Wanda hakan ya sa Gwamnan Ahmed Fintiri ya rasa yadda zai yi face saka ta, a cikin mamba a hukumar (BoT).
Kazalika ya ce, Ficewar wani Mamba a jam’iya ba abu ne mai dadi ba, Amma gudunmawar da tsohuwar Sanatan ta bayar a Jam’iyar, na kashin kanta ne kawai.
” Son ran Sanata Bent ya sa muka rasa wani Jigo a yankin ta Mr Filex Tangwami ” inji shi.
“Tun a shekarar 2019 lokacin da Sanata Bent ta yi rashin nasara, a hannun Binos Dauda, bata ta ba bada wani gudunma wa a Jam’iyar ba” a cewar shi.
” Ta yi wa jam’iyar PDP zagon kasa na tsawon shekaru biyu, don haka ba bu wani danasa ni, da jam’iyar PDP zata yi na rashin ta” inji shi.
Lokacin da ta ke jawabi a wurin bikin sauya shekar ta , Sanata Bent ta ce, ta bude sabon babi a rayuwar ta, na siyasa, biyo bayan komawar ta jam’iyar APC Mai Mulki.