Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, (LP), Peter Obi ya cire haramtacciyyar ƙungiyar nan ta ƴan awaren ƙabilar Ibo daga cikin jerin ƙungiyoyin ta’addanci na Najeriya.
Ɗan takarar na jam’iyyar Labour Party yace a shirye yake da bada gudunmawar sa wajen samun haɗin kan Najeriya sannan ya nuna rashin jindaɗin sa kan yadda rashin aikin yi, talauci, rashin adalci ke ƙara yawaita a ƙasar nan. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tuzuranci ya ƙare: Dattijo mau shekara 97 yayi wuff da wata matashiya ƴar shekara 30
Obi a cikin wani rubutu da yayi a shafin sa na Twitter, ya rubuta cewa:
“Najeriyar dake akan turba mai kyau tare da adalci, gaskiya da daidaito tabbas zata kawo ƙarshen irin ƙungiyoyin nan masu tsanani kamar su Boko Haram da ISWAP.”
Cire sunan ƙungiyar IPOB daga cikin ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya, bai zama abin mamaki ba ga masu sukar sa da ƴan adawa waɗanda suke zargin sa a matsayin wani mai yin kunnen uwar shegu kan abubuwan da ƴan awaren ke yi a ƙasar nan.
Ko a baya ma, ɗan takarar ya taɓa cewa mambobin ƙungiyar IPOB ba ƴan ta’adda bane, sai dai wasu ƴan Najeriya ba suji daɗin wannan furucin na sa ba.
Hakan ya sanya yayi wani rubutu inda ya kare maganar da tayi.
“Abu ɗaya da ban yarda da shi ba shine kiran ƴan IPOB da ƴan ta’adda. Ba ƴan ta’adda bane. Waɗanda suka yanke wannan hukuncin na iya yiwuwa suna da wani bayani wanda ni bani da shi.” A cewar sa
Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Sha Alwashin Kawo Karshen Shaye-Shayen Muggan Kwayoyi
A wani labarin na daban kuma, wani ɗan takarar gwamnan jam’iyyar PDP yasha alwashin kawo ƙarshen ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
A kokarinsa na tabbatar da dorewar matakan da gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta dauka na kawar da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a jihar, dan takarar gwamnan jihar Sokoto karkashin jam’iyyar PDP, Malam Sa’idu Umar FCNA. ya sha alwashin ci gaba da yaki da wannan barazana.
Dan takarar gwamnan jihar wanda kuma ke rike da sarautar gargajiya na Mallam Ubandoman Sokoto ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da ofishin cibiyar wayar da kan jama’a kan sha da fataucin miyagun kwayoyi (CESADA Sokoto) wanda Alh Abdulrazak Shehu,babban kwamishina na hukumar ma’aikatan jihar Sokoto ya kafa.