Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta binciki harin bam da ya faru a jihar Kaduna a ranar 3 ga watan Disamba.
Obi ya yi wannan kiran ne a ranar Talata lokacin da ya ziyarci kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar, inda sojojin Najeriya suka kashe sama da mutane 120 bisa kuskure.
Karanta nanRashin Iya Mulki Ne Ya Janyo Yan Majalisu 27 Barin PDP-Jam’iyar APC Reshen Jahar Ribas
Ya kasance a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke babban birnin jihar, inda ya gana da wadanda suka jikkata da suka samu raunuka a rikicin.
Tsohon gwamnan na Anambra ya koka da cewa kawo yanzu kasar nan ta samu tashin bama-bamai 16 da sojoji suka yi a bazata, wadanda suka hallaka sama da mutane 500, ba tare da wani abu da gwamnatin tarayya ta yi ba wajen dakile sake afkuwar irin wadannan bala’o’i.
Obi, ya kuma jaddada bukatar gwamnati ta tallafa wa sojoji don ganin ba a sake samun aukuwar lamarin kamar tashin bama-bamai na bazata daga yanzu.
Ya ce isassun kudade ga sojoji yana da matukar muhimmanci wajen tinkarar kalubalen tsaron a kasar domin a gujewa faruwar haka a Kaduna dama kasa baki daya.
A wani labarin kumaZa A Kashe Miliyan Uku Ga Duk Gida Guda,Da Za A Tsugunar Da Yan Gudun Hijira-Minista
A ranar Talata ne ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dakta Betta Edu, ta duba gidajen da ake ginawa ‘yan gudun hijira a yankin Idu da ke babban birnin tarayya Abuja.
Edu ta ce, za a gina gidajen mai daki daya da daki biyu ne domin karbar ‘yan gudun hijira a jihohi a wani bangare na kokarin shawo kan matsalar talauci a kasar nan.