Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Ribas ta ce rashin shugabanci nagari a jihar ne ya sa ‘yan majalisar dokokin jihar su 27 suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Fatakwal, ya ce wasu ‘yan majalisar dokokin jihar sun aminta da shi.
Karanta nanSojojin ruwa sun kama mutane 28 da ake zargin barayin mai ne a Ondo
Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas su 27 sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP a ranar Litinin din da ta gabata.
‘Yan majalisar wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, na karkashin bangaren kakakin majalisar, Martins Amaewhule, da ke biyayya ga ministan babban birnin tarayya (FCT).
Da yake mayar da martani kan wannan ci gaba, Okocha ya bayyana ficewar ‘yan majalisar dokokin jihar a matsayin gagarumar riba ga APC.
Okocha wanda kuma shi ne wakilin jihar Ribas a hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC), ya bayyana cewa an sanar da jam’iyyar a jihar a hukumance kan ficewar ‘yan majalisar zuwa jam’iyyar.
Okocha ya yabawa ‘yan Majalisar da suka sauya sheka.
Okocha ya ce gwamnati mai ci a jihar an gina ta ne a kan tubali amma ya lura cewa ayyukan gwamna (Fubara), yana cikin wani yanayi na rashin tabbas.
A wani labarin kumaRikicin Ribas: Ka fice daga PDP, ka dawo Jam’iyyar mu – APC ta zaburar da Wike
Ya kara da cewa babu abin da ke faruwa a jihar, yana mai cewa,akwai yunwa a kasa.
A cewar Okocha, sauya shekar ‘yan majalisar 27 za ta taka rawar gani a cikin gwamnati, inda ya ce wannan shi ne mafi kyawun hukunci da ‘yan majalisar suka dauka, duk da cewa wasu sun ce an makara.
Ya ce mun yaba musu kuma mun karbe su da hannu bibbiyu zuwa babbar jam’iyarmu mai farin jini.