Portugal vs Nigeria: Dalilin da yasa Osimhen ba zai buga wa Super Eagles wasa ba – Peseiro
Babban kocin Najeriya, Jose Peseiro ya ce bai ji dadin yadda Victor Osimhen ba zai buga wasan sada zumuntar da kasar za ta yi da Portugal ranar Alhamis.
Peseiro, da yake magana da Manema Labarai, ya bayyana cewa ya samu rahoto daga likitocin Napoli cewa Osimhen na fama da matsalar baya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu ya gana da Ƴan Kasuwa gabanin yaƙin Neman Zaɓe a Imo
Ba a sa ran dan wasan mai shekaru 23 zai samu lafiya nan da wasu makonni biyu.
Rahotanni daga kafafen yada labaran Italiya sun nuna cewa Osimhen ba shi da wata matsala ta jiki kuma dan wasan ya fasa buga wasan sada zumunci da Portugal domin kaucewa hadurran da ba dole ba.
Amma Peseiro yanzu ya matsa don saita tarihi.
“Likitan daga Napoli ya aika da rahoto ga likitan mu (Kungiyar Najeriya) cewa bayan wasan (da Udinese), Osimhen ya ji zafi a bayansa. Kuma cewa yana buƙatar tsakanin kwanaki 10 zuwa 15 don murmurewa.
“Men zan iya yi? Tabbas, ina son yin wasa da Osimhen. Dan wasa ne mai ban mamaki. Ina son yin wasa tare da mafi kyawun ‘yan wasa.
“Ban ji dadin hakan ba. Amma yanzu ba na tunanin Victor Osimhen. A gare ni, mafi mahimmanci shine ‘yan wasan da nake da su a nan,” in ji Peseiro.
Osimhen bai buga ko daya daga cikin wasanni uku na sada zumunci ba – Ecuador, Mexico, Algeria – da Super Eagles ta buga a karkashin Jose.
A wani labarin kuma: Tinubu zai kawo ƙuri’un Inyamurai dana yankin Kudu-maso-Gabas – Umahi
Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ba da tabbacin cewa jam’iyyar All Progressives Congress, APC, da ɗan takarar shugaban kasa, Bola Tinubu za ta cinye ƙuri’un ‘yan kabilar Igbo idan aka zabe shi.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake kaddamar da masaukin Gwamnan Ebonyi a ranar Laraba a Abuja.