Putin ya tattauna ta wayar tarho da shugaban rikon kwarya na Mali
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da shugaban rikon kwarya na Mali Assimi Goita, in ji Kremlin a ranar Talata.
A cikin wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar ta ce “A shirin na bangaren Mali, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar na rikon kwarya na Mali Assimi Goita.”
KARANTA WANNAN LABARIN:Masu Gidajen Burodi Na Kokawa Akan Tsadar Kayan Aiki
Sanarwar ta kara da cewa an mai da hankali musamman kan halin da ake ciki a yankin Sahara-Sahel.
Musamman bangarorin sun yi nuni da mahimmancin warware al’amura a Nijar ta hanyar siyasa da diflomasiyya kawai cikin lumana.
A halin da ake ciki, Mista Goita ya tabbatar da tattaunawa da Putin ta wayar tarho game da halin da ake ciki a Nijar, inda sojoji suka kwace mulki a wani juyin mulki a watan jiya.
Mista Putin “ya jaddada mahimmancin warware matsalar cikin lumana don samar da kwanciyar hankali a yankin Sahel,” in ji Mista Goita a dandalin sada zumunta na X, wanda aka fi sani da Twitter.
Kasashen yammacin Turai na fargabar cewa Nijar za ta iya tafiya daidai da makwabciyarta Mali, wadda shugabanninta suka dauki hayar sojojin haya daga kungiyar Wagner ta Rasha domin taimaka musu wajen yaki bayan da suka hambarar da gwamnatin dimokaradiyya shekaru uku da suka wuce tare da korar sojojin Faransa.
Mista Putin ya yi kira da a koma kan tsarin mulki a Nijar, yayin da shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi maraba da juyin mulkin.
Da alama goyon bayan Rasha na karuwa a Nijar tun bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli, inda magoya bayan gwamnatin mulkin sojan kasar suka daga tutocin kasar Rasha a wasu taruka da dama.
A wani labarin kuma:Masu Gidajen Burodi Na Kokawa Akan Tsadar Kayan Aiki
Shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin, ya sha alwashin tallafawa duk wata kasa da ta kuduri aniyar kare muradunta na kasa a kan kasashen yammacin duniya.
Putin ya ce Moscow za ta hada kai da kowace kasa a fannin fasaha.