Zamu Goyi Bayan Duk Wata Ƙasa Da Ke Son Kare Kanta – Shugaban Rasha, Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin, ya sha alwashin tallafawa duk wata kasa da ta kuduri aniyar kare muradunta na kasa a kan kasashen yammacin duniya.
Putin ya ce Moscow za ta hada kai da kowace kasa a fannin fasaha.
KARANTA WANNAN LABARIN:Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen janye ƙarar da ta shigar da Emefiele
Ya jaddada cewa, Rasha ta kuduri aniyar yin aiki tukuru a kan dangantakar hadin gwiwa da ake da su, da kuma samar da sabbin dangantakar da ke bisa la’akari da nasarorin da ta samu na tsawon shekaru da ta samu a fannin hadin gwiwar moriyar juna.
A cikin sakon da ya aike wa mahalarta taron na rundunar soja ta 2023, Putin ya ce: “Rasha a shirye take ta kara zurfafa hadin gwiwar fasaha da hadin gwiwar tsaro da sauran kasashe, wato tare da duk wadanda ke neman kare muradun kasa da tafarkin ci gaba mai cin gashin kai, yana da matukar muhimmanci a yi kokarin hadin gwiwa don gina tsarin daidaito da tsaro wanda ba za a iya raba shi ba wanda zai kare kowace kasa”
Kalaman Putin na zuwa ne a lokacin da sojoji suka hambarar da zababbiyar gwamnati a Jamhuriyar Nijar.
Akwai rahotannin da ke cewa Rasha na goyon bayan gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Tarayya ta fara shirye-shiryen janye ƙarar da ta shigar da Emefiele
Gwamnatin tarayya ta nemi a janye karar ‘mallakar makamai ba bisa ka’ida ba’ da ta shigar a kan gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele da aka dakatar a babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas.
Daraktan shigar da kara na ma’aikatar shari’a ta tarayya Mohammed Abubakar ya shaida wa mai shari’a Nicholas Oweibo cewa bukatar ta biyo bayan sakamakon ci gaba da bincike da gwamnati ta yi.