Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zuwa wani taro a ranar Laraba a Abuja, kamar yadda majiya mai tushe da ke da masaniya kan tafiyar ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN.
Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC ya gayyaci Malam Shekarau, wanda shine dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP, zuwa wurin taron domin janye shi zuwa cikin jam’iyyar APC.
Rahotanni sun ce tuni Malam Shekarau ya cimma matsaya da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan ya koma jam’iyyar da kuma jagorantar yakin neman zabensa a yankin Arewa maso Yamma.
Wani jigo a jam’iyyar PDP a Kano ya shaida wa jaridar cewa jam’iyyar ta fara tattaunawa a kan gyara tsarin da za ta yi wa Malam Shekarau.
A cewarsa, guda cikin jihar jigan jam’iyyar a Kano Bello Hayatu Gwarzo, ya sanar da jiga-jigan jam’iyyar a jihar game da zuwan Malam Shekarau da shirin karbar abokan tafiyarsa.
Daily Nigeria ta samu tabbacin cewa abokin takarar Mista Tinubu, Kashim Shettima, ya gana da Malam Shekarau a ranar 8 ga watan Agusta, amma majiyoyin sun ce “ba a cimma yarjejeniyar komai ba”.
Duk da cewa masu lura da al’amura sun ce tsohon gwamnan ya riga ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP, amma shi s bisa ka’ida ya gayyaci majalisarsa ta shura, domin ta ba shi shawara.Ana sa ran majalisar za ta gabatar da rahoto a yau kuma za a sanar da yanke shawara a cikin mako.