Wani yaro dan shekara 16 mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a kauyen Kuki da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa har yanzu ba a gano dalilan daya sanya yaron ya kashe kansa ba.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, Hakimin Bebeji ya fitar, ya mika rahoton afkuwar lamarin ga mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, a yayin taron majalisar masarautar a ranar Litinin din da ta gabata.
Matawalle Ya Rattaba Hannu kan Dokar Hukuncin Kisa Ga Wasu Mutane
Ya bayyana cewa, Sarkin ya ba da umarnin a kai rahoton ga ‘yan sanda da ke masarautar domin gudanar da bincike mai zurfi kan musabbabin mutuwar yaron.
Sai dai da aka tuntubi jami’in dan jin karin bayani kan lamarin, ya shaida wa wakilinmu cewa hakimin kauyen ya yi wa mahaifin marigayin tambayoyi kan ko yaron yana shan kwayoyi ne ko kuma tabin hankali.
Ya kuma kara da cewa sarkin ya umarci hakiman karamar hukumar da su gudanar da addu’o’i masu yawa domin gujewa faruwar irin wannan lamari anan gaba.
Har kawo lokacin hada wannan labari bamu samu ji daga bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ba.