Chief Dan Orbih, mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP reshen Kudu maso Kudu ya ce raba kasarnan da ballewar wani bangare na kasarnan ba shi ne mafita ba daga matsalolin da kasar ke fuskanta.
Mataimakin shugaban Jam’iyyar PDP din ya bayyana hakan ne a yayin zantawarsa da manema labarai a ranar Lahadi.
Ya kara da cewa damuwar da ‘yan kasar ke nuna wa yana da alaka da rashin kyakkyawan shugabanci na ‘yan siyasa. Wanda ya ce hakan ne ya sanya wasu daga cikin ‘yan kasar ke fafutikar ballewa daga kasar.
Orbih, ya ce kasar za ta samu ci gaba ne kawai idan aka samu kyakkyawan tsarin shugabanci da za a yi amfani da shi wajen tattalin arzikin kasar.
Orbih ya ce kasar za ta zama kasa guda ce da kyakkyawan shugabanci.