Rabon Tallafin Abinci: An Raunata Kwamishiniyar Harkokin Mata
A ƙarshen makon nan ne aka kai wa Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jihar Ondo, Dakta (Mrs) Olubunmi Osadahun hari a yankin Arigidi Akoko da ke Jihar a yayin rabon kayan abinci domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur da Gwamnati ta yi.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne suka kai wa Kwamishiniyar hari a yankin karamar hukumar sakamakon zargin cewa jami’an Gwamnati sun ɓoye wasu kayayyakin a yayin rabon.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani mutum ya yi amfani da wata kujera mai launin shuɗi don kai wa Kwamishiniyar hari.
Kwamishiniyar ta samu rauni yayin harin kuma tuni aka garzaya da ita asibiti domin kula da lafiyarta.
KARANTA NAN:Satar Ɗanyen Mai: Dakarun Sojin sama sun lalata Haramtattun matatun mai guda 7 a Rivers
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa “mutumin wanda dan jam’iyyar APC ne a Arigidi da ke Akoko ta Arewa, ya halarci wurin a yayin da ake ci gaba da rabon kayan abincin a yankin”.
“Ba mu san abin da ya faru tsakaninsa da Kwamishiniyar ba, sai kawai muka gan shi a lokacin ya ɗauki daya daga cikin kujerun ya buga a bisa kan Kwamishiniyar”.
“Dukan da yayi sanadiyar samun rauni mai zurfi a kanta kenan”.
“Nan take dai wasu matasa maza masu goyon bayan Kwamishiniyar suma suka hau kan maharin domin ɗaukar fansa”.
A wata hira da wata mata da ta ce ita ce ‘yar Kwamishiniyar Mrs Jumoke Bakare ta shaida wa Majiyar Dimokuraɗiyya cewa tuni aka kwantar da mahaifiyarta a asibiti bayan harin.
A cewarta “Mahaifiyata tana asibiti, ba za ta iya magana da wakilanmu ba domin yanzu tana cikin yanayin hutawa.
Idan za ku tuna cewa Gwamnatin Jihar dai ta fara rabon kayan tallafin abinci ga al’ummar Jihar.
Gwamna Rotimi Akeredolu wanda ya samu wakilcin kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a Mrs Bamidele Ademola Olateju ya bayyana haka a hedikwatar Isua na karamar hukumar Akoko ta Kudu maso gabas na Jihar ya ce za’a raba buhunan shinkafa 1,200 ga mafidanta 6,000 na karamar hukumar.
Ya ce shirin Tallafin za a bayar da shi ne ga duk mazauna Jihar ba tare da la’akari da bambanci siyasa ba.
Idan kuma za a iya tunawa, bayan fara rabon kayan tallafin ne gamayyar kungiyoyin farar hula a Jihar suka koka kan badakalar da suka ce anyi wajen rabon kayan abinci a faɗin Jihar.
Sun yi zargin cewa rabon kayan anyi shi ne a lullube cikin sirri ba kowa ne yasan anayi ba.
Zargin na ƙunshe ne a cikin wata Sanarwa da kungiyar ta fitar kuma mai ɗauke da sa hannun Manyan Jagororin kungiyar Franklin Oloniju, da Pius Akomolafe Alo, da Martins Stella, da Ikeokwu Emmanuel Daramola da Bola Fasuyi da suka bayyanawa manema labarai a Akure babban birnin Jihar.
A cewarsu “Gamayyar kungiyoyin farar hula a Jihar Ondo sun nuna rashin jin dadin su da yadda Gwamnatin Jihar Ondo ke tafiyar da rabon kayan abinci a Jihar.