Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan makarantun kwana na Sakandire da na firamare da masu zaman kansu da su rufe hutun zangon farko a ranar Juma’a 15 ga Disamba, 2023 inda za a ci gaba da hutun har zuwa ranar Asabar 16 ga Disamba, 2023.
An bukaci iyaye da masu kula da daliban da ke makarantun kwana da su zo su dauki ‘ya’yansu a safiyar ranar Asabar 16 ga watan Disamba.
Karanta nanDaga Karshe Gwamna Akerodolu Ya Amince Da Baiwa Mataimakinsa Rikon Kwarya
Daliban makarantar kwana za su koma makaranta ranar Lahadi, 7 ga Janairu, 2024, yayin da dalibanda ba na makarantar kwana ba za su koma makaranta ranar Litinin, 8 ga Janairu, 2024.
Kwamishinan ilimi na jihar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya bukaci iyaye da masu kula da yara da su da su tabbatar ‘ya’yansu sun cika wa’adin da aka amince da su na komawa makaranta.
Ya kuma yi gargadin cewa za a dauki matakin ladabtarwa ga duk dalibin da ya ki bin tsarin da aka tsara.
A wani labarin kumaZa A Kashe Miliyan Uku Ga Duk Gida Guda,Da Za A Tsugunar Da Yan Gudun Hijira-Minista
Kwamishinan ya bayyana jin dadinsa da irin hadin kai da goyon bayan da ma’aikatar ilimi ta samu tare da yi wa daukacin dalibai da almajirai fatan a yi hutu lafiya.
Sanarwar ta kara da cewa Iyaye/Masu kula da Almajirai da Dalibai a makarantun allo za su isar da sassansu zuwa gida da sanyin safiyar Asabar 16 ga Disamba 2023.
Dalibai za su koma makarantunsu a ranar Lahadi 7 ga Janairu, 2024 yayin da za a ci gaba da karatu a ranar Litinin 8 ga Janairu, 2024.