- Majalisar dattawa ta bayyana bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na neman a tantance kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa 19
- Tuni Majalisar Dattawan ta umurci hukumar da ke kula da tantancewa ta kasa da ta dawo Bakin Aiki nan da makwanni biyu
- A Kwanakin baya Ne dai Shugaban Kasa Tinubu ya nada kwamishinonin na NPC su 19
Majalisar dattawa a ranar Talata ta bayyana bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na neman a tantance kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa 19.
Tinubu ya kuma bukaci a tabbatar da sunayen Bashir Indabawa (Arewa-maso-Yamma), Enorense Amadasu (Kudu-maso-Kudu), da Babajide Fasina (Kudu maso Yamma) a matsayin kwamishinonin Hukumar.
KARANTA WANNAN: KARANTA WANNAN: Rikicin Rivers: Ka Ayyana kujerun ‘Yan Majalisa 27 a Matsayin Babu Kowa – LP Ga Shugaban Majalisa
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya karanta bukatar Tinubu a zaman majalisar a ranar Talata sannan ya umurci hukumar da ke kula da tantancewa ta kasa da ta dawo nan da makwanni biyu.
Sai dai Majalisar Dattawa ta amince da nadin Ambasada Desmond Akawor a matsayin kwamishina mai wakiltar jihar Ribas a bangaren tattara kudaden shiga bayan rasuwar tsohon kwamishinan gwamnatin tarayya na RMAFC daga jihar Rivers, Asondu Temple.
Sunaye da jihohin da aka nada kwamishinonin NPC sun hada da:
1. Emmanuel Eke (Abia)
2. Clifford Zirra (Adamawa)
3. Chidi Ezeoke (Anambra)
4. Isa Buratai (Borno)
5. Alex Ukam (Cross River)
6. Blessyn Brume-Ataguba (Delta)
7. Jeremiah Nwankwegu (Ebonyi)
8. Tony Aiyejina (Edo)
9. Ejike Ezeh (Enugu)
10. Abubakar Damburam (Gombe)
11. Uba Nnabue (Imo)
12. Dogon Garba (Kaduna)
13. Aminu Tsanyawa (Kano)
14. Yori Afolabi (Kogi)
15. Olakunle Sobukola (Ogun)
16. Temitayo Oluwatuyi (Ondo)
17. Maryama Afan (Plateau)
18. Ogiri Henry (Rivers
19. Sanay Sale (Taraba)
A wani labarin kuma,Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Muhimman Hakkokin Emefiele
Mai shari’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya ya sanya ranar yanke hukunci kan aiwatar da wasu muhimman kararrakin da tsohon gwamnan CBN Emefiele ya shigar
Alkalin kotun ya tsayar da ranar ne bayan ya saurari bahasi daga bangarorin da ke karar
Tsohon Gwamnan na CBN ya shigar da Kara kan tauye masa Hakkokin Sa na rayuwa
Mai shari’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya a ranar Litinin ya sanya ranar 8 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan aiwatar da wasu muhimman kararrakin da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya shigar.
Alkalin ya tsayar da ranar ne bayan ya saurari bahasi daga bangarorin da ke karar