-Dole ne a saki zakzaky, kuma a kori manyan jamián tsaron najeriya.
In ji gamayyar kungiyoyin juyin-juya hali.
Inuwar Kungiyoyi daban-daban, masu yunkurin kawo juyi a Najeriya, domin ceto talakawa da matasa, sun bayyana cewa za su soma gudanar da zanga zanga a Abuja babu kakkautawa daga ranar Litini mai zuwa.
A wata takardar bayan taro da Olaseni Ajayi ya rattatawa hannu, a madadin Kungiyoyin da su ka hada da ýan siyasa, ma’aikata da matasa da kungiyoyin farar hula, sun aminta da cewa idan ba gaba daya ýan Najeriya sun tashi tsaye sun kawo karshen mulkin kama karya na Gwamnatin Buhari ba, to abin zai wuce gona da iri.
‘’Sanin kuwa ne cewa masu tafiyar da mulkin Najeriya, wadanda su ka hada da ýan Jamíyyar PDP da APC a dukkanin matakan gwamnati, ba za su iya fitar da kasar nan daga kangin da su ka jefa ta a ciki ba’’. In ji su.
Takardar bayan taronsu ta cigaba da cewa akwai matsalolin rashin tsaro masu yawa a Najeriya, da kashe kashe mutane da yawaitar ýan gudun hijira. Wannan na nuna cewa Najeriya ta kama hanyar rushewa, saboda kama karya da zalunci na kara habaka.
Gwamnatin Buhari, babu abin da ta kawo wa kasa, sai jami’anta da su ke dibgar sata da durkusar da tattalin arziki.
Su ka ce, wannan ne ya sa ya zama wajibi ga matasa da sauran Ýan Najeriya, mu fantsama akan tituna daga ranar Litini mai zuwa, 5 ga watan Agusta.
Daga nan su ka ce wadannan gamayyar kungiyoyi su ne za su jagoranci zanga zangar, wacce ke kunshe da bukatu guda biyar a madadin sauran ýan Najeriya.
Dole ne a cire dukkanin tsare tsaren bankin duniya daga tsarin tattalin arzikin Najeriya, wadanda su ka haifar da karin kudin man fetur da wutar lantarki.
Dole a dauki matakai na gaske wajen kawo karshen kashe jamaá da kai hare hare. Kuma dole ne a kori manyan jamián tsaro.
Sannan dole a saki dukkanin fursunonin siyasa, cikinsu har da Shaik Zakzaky.
Dole a soma aiwatar da sabon tsarin albashi na naira dubu talatin.
Dole ne a rage kudin makaranta.