Ranar tunawa da mazan jiya: Ku Inganta jin dadin jami’an soji – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ga FG
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa kokarin da take yi na ganin an inganta walwalar jami’an soji.
Lawan, wanda a halin yanzu yake shugabantar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, a sakon da ya aike don tunawa da ranar tunawa da sojojin kasar ta shekarar 2024, ya ce taron na shekara-shekara na tunawa da mazan jiya da suka sadaukar da rayuwar su don zaman lafiyar al’umma da kuma ranar yin tunani kan muhimmancin zaman lafiya da hadin kai.
KARANTA WANNAN LABARIN:2027: Dalilin da yasa Atiku, Peter Obi, Kwankwaso suka yi maja – Pat Utomi
Tsohon shugaban majalisar dattawan, ya bukaci ‘yan Najeriya da su marawa kokarin da rundunar sojin kasar ke yi na gina kasa da duk ‘yan kasar ke samun kwanciyar hankali.
Ya ce, “A wannan gagarumin biki, na bi sahun ‘yan Nijeriya maza da mata da suka yi hidima da kuma ci gaba da yi wa al’ummarmu hidima da jajircewa da sadaukarwa.
“Muna girmama abubuwan tunawa da wadanda suka sadaukar da rayukansu don kare ‘yancinmu da tsaronmu. Ba za a taɓa mantawa da sadaukarwarsu ta ƙarshe ba.
“Wannan taron na shekara-shekara yana kasancewa a matsayin tunatarwa mai mahimmanci na farashin da aka biya don zaman lafiya da kwanciyar hankali. Rana ce ta yin tunani a kan sadaukarwar da jami’an sojanmu da iyalansu suka yi.
“Yayin da muke tunawa da jaruman mu da suka mutu, dole ne mu amince da kalubale da matsalolin da sojojin mu ke ci gaba da fuskanta. Sojojin mu sun cancanci goyon bayanmu, ba a wannan rana kadai ba amma duk shekara.
“Ina yabawa gwamnatin tarayya bisa kokarinta na inganta jin dadi da yanayin jami’an sojin mu. Sai dai akwai bukatar a kara kaimi wajen magance bukatun Sojojin mu da kuma tabbatar da cewa sun samu kayan aiki da tallafin da suke bukata domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
“Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ci gaba da saka hannun jari a fannin horaswa, kayan aiki, da kayayyakin more rayuwa ga Sojojin mu. Dole ne kuma mu tabbatar da cewa jami’an sojanmu sun sami isassun diyya, fa’idodi, da ayyukan tallafi
A wani labarin kuma:Kada ka kuskura ka tsaya takarar shugaban kasa a 2027’ – PDP ga Atiku
Wata kungiya mai matsa lamba a cikin jam’iyyar PDP, wato Concerned PDP League, CPDPL, ta yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023, da kada ya sake tsayawa takara a 2027.
Shawarar kungiyar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka sanya wa hannu a ranar Lahadi kuma ta fitar a Abuja ta hannun sakatarenta na kasa, Alhaji Tasiu Muhammed da kuma mukaddashin daraktan yada labarai da sadarwa na kasa, Gbenga Adedamola.