Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana rantsar da gwamnan jihar Osun Ademola Adeleke a matsayin wani haske ga Kasar nan daga cikin duhun rashin shugabanci da take ciki.
Atiku Wazirin Adamawa ya ce rantsar da Sanata Ademola ya wuce nasara ga mutanen jihar Osun.
KU KARANTA KUMA Ni Da Okowa Muna Tattaunawa Da Yan Kasuwa Domin Farfado Da Najeriya — Atiku
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Tsohon mataimakin shugaban Kasar ya taya gwamnan murnar rantsar da shi da aka yi a yau Lahadi a matsayin gwamna H.E. Ademola Adeleke.
Atiku wanda bayan rantsar da gwamnan ya daga hannunsa a gaban dimbin mutanen da suka halarci bikin ratsarwa.
“Magarin haska Osun ne a yau kuma wata alama ce ta farfado da kasar nan daga cikin duhun rashin jagoranci da shugabanci.
“Bikin rantsar da Sanata Ademola Adeleke ya wuce nasara ga mutanen jihar Osun“.
Ga wasu hotuna a kasa
A Wani Labarin Kuma Maitaimakawa Buhari Ya Yi Murna Da Ficewar Ningi Daga Jam’iyyar NNPP
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan kafafen yada labarai na zamani, Bashir Ahmad, ya yi murnar ficewar ma’ajin jam’iyyar NNPP, Shehu Ningi, daga jam’iyyar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Ningi a cikin wata wasika da ya rubuta wa shugaban jam’iyyar na NNPP mai kwanan watan ranar 25 ga watan Nuwambar 2022, ya ce ya yanke shawarar barin mukaminsa na ma’aji na kasa da kuma zama mamban jam’iyyar “saboda wasu dalilai.”