Kungiyar Malaman Kwalejijojin Kimiya da Fasaha ta Kasa ASUP ta tsunduma wani yajin aikin sai babanta gani.
Shugaban Kungiyar ta Kasa Anderson Ezeibe shine ya shaida wannan labari wa manema labarai a yau talata a birnin tarayya Abuja.
Ya ce daga yau mambobin kungiyar ba za su sake zuwa Makarantu ba har sai gwamnati ta biya musu bukatunsu.
Wannan mataki da kungiyar ta dauka na zuwa ne duk irin yunkurin gwamnati na dakile yajin aikin.