Gabanin shari’ar da ake yi wa dan jaridar Amurka Evan Gershkovich, wanda aka kama a watan Maris bisa zarginsa da laifin leken asiri, Rasha ta tsawaita wa’adin tsare shi a gidan yari na watanni uku. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Wata kotu ce ta bayar da umarnin a tsawaita tsare Mr Gershkovich har zuwa ranar 30 ga watan Agusta, kamar yadda kafafen yada labaran Rasha suka rawaito.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bankuna Yanzu Zasu Iya Bayar Da Katin Ƙasa – FG
Jami’an Amurka sun yi kira da a gaggauta sakin wakilin jaridar Wall Street Journal.
Kama shi dai shi ne karo na farko da Moscow ta zargi wani dan jaridan Amurka da leken asiri tun zamanin Gwamantin tarayyar Soviet.
Mista Gershkovich, wanda aka kama a lokacin da yake bayar da rahoto kan yakin Ukraine, ya musanta zargin, kamar yadda jaridar Wall Street Journal da gwamnatin Amurka suka yi.
Hukuncin da alkalin ya yanke na nufin za a ci gaba da tsare shi a gidan yarin dake birnin Moscow, kafin cigaba da sauraron shiri’ar.
A wani labarin kuma, Bankuna Yanzu Zasu Iya Bayar Da Katin Ƙasa – FG
Gwamnatin Tarayya ta ce a yanzu ‘yan Najeriya zasu iya neman bankunan kasuwancinsu da su ba su katin cirar kudi wanda yake dauke da katin shaidar zama dan kasa, wato kati guda da zai yi aiki biyu, cirar kudi da nan kuma ya zama katin dan kasa.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, wanda ya bayyana hakan a Abuja, ya ce an samu amincewar ne a taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC)