An dage shari’ar dan kasar Chanan da ake zargi da kashe budurwarsa mai suna, Ummukulsum Sani Buhari, wadda aka fi sani da Ummita a jihar Kano.
An dai dage zaman kotun ne har zuwa ranar 27 ga watan Oktoba, wato dai zuwa lokacin da za samarwa da Mr. Geng Quangrong, wanda zai yi masa tafinta daga turanci zuwa Yarensa na Chanisanci.
KARANTA ANAN: Buhari Zai Gabatar Da Kasafin kudin Shekarar 2023
Jim kadan da fara zaman kotun aka dage zaman saboda matsalar rashin fahimtar bayanai daga bangaren Mista Geng, wanda ake zargi da kisan Ummukulsum Sani Buhari, da aka fi sani da Ummita, a Kano.
A watan da ya gabata ne dai ake zargin Dan Chanan da zuwa har gidan su Ummita, tare da hallakata a unguwar Janbulo.
A wani labarin kuma: NSCDC ta cafke wani Matashi kan Fashi da Makami a Nasarawa
Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (NSCDC) reshen jihar Nasarawa sun kama wani matashi dan shekara 18 mai suna Muhammed Hussaini da ake zargin yana addabar mazauna karamar hukumar Lafia ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, Mista Jerry Victor, wanda ya yi faretin Hussaini, ya ce shi da ‘yan kungiyarsa sun kai hari kan wasu yara maza da ke kiwon shanu a bayan gidan gwamnati da ke Lafia da wata karamar bindiga ta gida inda suka gudu, suka ci karfinsu.
Ya ce mai shanun ya kai rahoton lamarin ga rundunar a ranar 17 ga watan Agusta, kuma jami’an rundunar sun kai dauki tare da kama wanda ake zargin.