Rahotanni na nuna cewa, an yi garkuwa da mutane takwas a kauyen Madauchi da ke kusa da yankin Birnin Yero a karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin wanda ya zanta da DAILY POST a Kaduna a ranar Litinin Malam Nasir Ibrahim ya ce yankin ya zama maboyar ‘yan ta’adda a ‘yan kwanakin nan.
Ya ce wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane bakwai a Ungwan Mallam, da ke yankin unguwar kwana biyu da suka wuce.
“A cikin wannan yankin, babu masu hannu da shuni. Mu duka manoma ne masu Neman abinci. Yawancin mazauna yankinmu suna fuskantar wahalar cin abinci ko da sau ɗaya a rana. Amma duk da haka, masu laifi, ‘yan fashi suna ta’addanci ga al’ummarmu.”
Wani shugaban al’ummar da ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen Mai suna Suleman Abdullahi ya ce ‘yan bindigar a daren Lahadi sun fara harbe-harbe a yankin.
Da yawa daga cikin mazauna yankin, ya ce, saboda harbin bindigar, sun kutsa cikin daji yayin da ‘yan fashin suka raunata wasu tare da tilasta musu shiga motar su.
Ya ce tun da aka tafi da mutanen garin ba a ji komi daga ‘yan fashin ko wadanda abin ya shafa ba.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su haskaka fitulun bincikensu a yankin domin ‘yan ta’adda suna yawan tsoratar da mazauna yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran wayarsa ba domin tabbatar da faruwar lamarin, kuma bai amsa sakon karta kwana da da aka aika masa ba.