Wasu daliban makarantun Firamare da Sakandare a jihar Kaduna, sun ki komawa makaranta domin gudanar da sabon zangon karatu saboda fargabar hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana ranar 4 ga watan Satumba, na 2022, a matsayin ranar da za a bude dukkan makarantun jihar domin gudanar da sabon zango, sai dai makonni biyu da komawa makaranta, har yanzu wasu dalibai ba su koma aji ba sakamakon ayyukan ‘yan ta’adda a cikin jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Duk da cewa gwamnati ta baiwa daliban tabbacin samun tsira, wasu iyayen na fargabar barin ‘ya’yansu su koma makaranta saboda babu wasu tsare-tsare na tsaro a wasu makarantun.
Suleiman Ibrahim, dalibin Sakandaren Gwamnati, Kakuri-Kaduna, ya ce ba zai iya kasada da ransa zuwa makaranta ba, saboda bai san lokacin da ‘yan bindiga za su kai hari ba.
Karanta kuma: Yan Bindiga Sun Sace Wasu Dalibai A Jihar Kaduna
Josephine Moses na Kwalejin Fasaha ta Gwamnati, da ke Malali, a Kaduna, ya ce ba zai je makaranta ba har sai gwamnatin jihar ta sanya matakan tsaro a makarantarsu.
“Kaɗan daga cikinmu ne kawai suke zuwa. Yawancin ajujuwa babu kowa a cikin su domin babu sauran daliban da suka amince su zo domin duk suna tsoron masu garkuwa da mutane,” inji shi
Jaridar Daily Post ta rawaito cewa, Moses Danjuma, dalibin aji 3 ne a babbar sakandure na makarantar Excel Schools, Kakuri-Kaduna, ya ce wurin da makarantar take daidai da yadda ake jan hankalin masu garkuwa da mutane ne, ya kuma yi kira ga mahukuntan makarantar da su koma wani wuri mai tsaro.
Sai dai wasu daga cikin daliban sun sha alwashin ci gaba da zama a gida har sai gwamnatin jihar ta dauki matakan tsaro.
A wani labarin kuma: Gwamnatin Tarayya Da ASUU: Kotu Ta Dage Cigaba Da Sauraren Karar
Kotun masana’antu ta kasa ta dage ci gaba da sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar tana kalubalantar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yi zuwa ranar Litinin 19 ga watan Satumba domin sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar.
A zaman da aka koma ranar Juma’ar nan, lauyan gwamnatin tarayya, James Igwe, ya bukaci kotun da ta gaggauta sauraron karar saboda gaggawar da aka yi domin baiwa dalibai damar komawa makaranta.