Rashin Tsaro: Matasan Arewa Sun Bukaci A Cire Monguno Daga Muƙamin sa
A ranar Laraba ne matasan Arewa karkashin kungiyar matasan Arewa (AYA) suka gudanar da zanga-zanga a babbar kofar majalisar dokokin kasar inda suka bukaci a tsige mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (Mai Ritaya) kan matsalar rashin tsaro a kasar.
Da yake jawabi ga Manema Labarai, Sakataren Yada Labarai na AYA, Aliyu Muhammed, ya ce Monguno ya gaza ba da damar hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen yaki da rashin tsaro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Komai da ya Shafe ka Karya ce – Bode George ya caccaki Tinubu
Idan za’a tuna an naɗa NSA a shekarar 2015 tare da tsoffin hafsoshin tsaro: Janar Abayomi Olonishakin (Babban Hafsan Tsaro), Laftanar-Janar. Tukur Buratai (Babban Hafsan Sojoji), Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (Babban Hafsan Sojan Ruwa), da Air Marshal Sadique Abubakar (Babban Hafsan Sojan Sama).
Sai dai a lokacin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara ya kasance Olonisakin da sauran hafsoshin tsaron kasar, aka kore su kan kasa shawo kan matsalar tsaro a ƙasar.
Mohammed ya ce, “ NSA ko dai bak baiwa shugaban kasa shawara ba ko kuma ra’ayoyinsa ba su da tasiri, don haka, da alama nasarar da ‘yan ta’adda suka yi a kan dakarun mu. Don haka muna kira daya gaggauta yin murabus ko kuma Buhari ya kore shi.
“Muna son a inganta tsaron kasar nan ba tare da wani sharadi ba daga halin da take ciki zuwa mai gamsarwa.
Shugaban matasan ya sha alwashin cewa kungiyar za ta hada kai tare da gudanar da gagarumar zanga-zanga a fadin jihohin Arewa 19 idan har shugaban kasa ya ki korar hukumar ta NSA zuwa ranar Juma’a.