By Abbas Yakubu Yaura
Kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji ta Red Cross ya yi gargadi kan karuwar cikas ga samar da kiwon lafiya saboda takurawa da rashin tsaro a fadin kasar.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta bayyana damuwarta a wani taron bita mai taken “Bayar da Lafiya a Hadari”, wanda aka shirya da ‘yan jaridu gami da Jami’an Kulawa da kimantawa na cibiyoyin kiwon lafiya a Awka, babban birnin Anambra a ranar Asabar, in ji Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Shugaban gudanarwa lafiya na ICRC,reshen Anambara Ms Constancia Amagba, tace haɗarin dake tattare da isar da lafiya ya haɗa da cin zarafi na zahiri da na baki wanda zai iya shafar jin daɗi ko daidaita tunanin ma’aikacin lafiya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Amagba yace an hana mutanen da ke bukatar kulawar lafiya saboda takunkumin hana motsi ciki har da aiwatar da dokar hana fita da zaman gida-gida.
Ta ce satar mutane da cin zarafin ma’aikatan kiwon lafiya sun lalata aikin tsarin tare da haifar da lahani ga marasa lafiya da masu rauni.
A cewarta, duk wani aiki na tashin hankali ko na zahiri ko toshewa ko barazanar tashin hankali da ke kawo cikas ga samun dama da isar da kaya ko ayyukan kiwon lafiya a lokacin gaggawa haɗari ne ga kiwon lafiya.
Kazalika Mai kula da lafiya yace babban abin daya fi damun ICRC shi ne maida martani na gaggawa ga ceton rayuka wanda hakki ne na kowa da kowa har da wadanda ake zargi.
Shi ma da yake magana, Mista Fidelis Ikeji, Jami’in Sadarwa na Red Cross a Anambra ya yi kira ga ‘yan jarida da su taimaka wajen fadakarwa da bayar da shawarwari don hana ma’aikatan kiwon lafiya shiga cikin marasa lafiya dake bukata.