Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN) na shirin gudanar da wani bikin noman shinkafa a Abuja domin tallafawa kokarin gwamnatin tarayya na samar da Isasshen abinci a fadin kasar nan, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ana sa ran za a gudanar da bikin a harabar cibiyar kasuwanci da masana’antu dake Babban Birnin Tarayya Abuja (ACCI), kuma tuni shirye-shiryen suka fara kankama, domin cimma nasarar gudanar da Babban taron.
A lokacin da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ziyarci wurin da ake shirin gudanar da Taron dake daura da titin filin jirgin, an hango cuncurindon Al’uma da suka yi taron kudan zuma a yayin da aka sauke tirelolin shinkafa da suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan.