Ma’aikatan hukumar gidan waya ta Najeriya NIPOST sun rufe babban ofishin hukumar da ke Abuja, domin nuna adawa da nadin da aka yi wa Tola Odeyemi a matsayin Chief Executive Officer/Postmaster-Janar.
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana a makon da ya gabata cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya canza shugabancin hukumomin sadarwa, ciki har da NIPOST.
Sai dai jim kadan bayan samun labarin nadin Odeyemi, an samu rahotannin cewa an mayar da Adeyemi Adepoju, wanda aka kora daga mukaminsa.
Karanta nanDaga Karshe Manyan Motocin Yan Majalisar Wakilai Sun Shigo Hannunsu
A cikin wani faifan bidiyo, an ga Adepoju yana jawabi ga wasu ma’aikata da suka yi ikirarin cewa Tinubu ya sake nada shi.
Tun da farko a wata sanarwa da NIPOST ta fitar a ranar Juma’a, Adepoju ya yi zargin cewa shugaban kasa Bola Ahmed ya sake nada shi a matsayin babban ma’aikacin gidan waya na tarayya da kuma babban jami’in hukumar gidan waya ta Najeriya NIPOST.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayarwa Rt. Honorabul Adeyemi Sunday Adepoju matsayinsa na babban ma’aikacin gidan waya na tarayya kuma babban jami’in hukumar ta NIPOST, inda ya bayar da misali da yadda Adepoju ya nuna kyakkyawan jagoranci da kyakkyawan aiki a lokacin zamansa a matsayin dalilin mayar da shi bakin aikin kamar yadda sanarwar da NIPOST ta fitar.
A wani labarin kumaJami’ar Gusau Ta Umarci Dalibanta Dake Zaune A Garin Damba Su Gaggauta Barin Wurin Baki Daya
Sai dai a ranar Litinin din nan ma’aikatan da suka yi zanga-zangar sun hana shiga sabuwar shugabar hukumar ta NIPOST, inda suka ce nadin nata ya saba wa burinsu.
Inda suka bayyana cewar ba ita shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya nada ba duba da cewar akwai tsoffin wadanda ke aiki a wurin da suka fi ta gogewa akan harkar sadarwa.