Majalisar Masu Ruwa da Tsaki ta Musulman Jahar Kwara a ranar Juma’a sun yi Allah wadai da kisan Habeeb Mustafa, Wanda aka kashe sakamakon rikicin sanya Hijabi a Makarantar Baptist dake Ijagbo a ranar Alhamis.
Sunyi wannan kiran ne a lokacin da suke yiwa manema labaru jawabi a Ilori akan faɗan daya faru a ranar Alhamis wanda yayi sanadiyar jikkata mutane da dama.
Gawar kamar yanda iyayen ta suka bayyana, tana ɗaya daga cikin wanda aka hana shiga Makarantar sakamakon sanya Hijabi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yanzu-yanzu: Majalisar Dokokin Zamfara Ta Sake Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
Habeed Mustafa ta shiga wata zanga-zangar lumana akan matakin wanda ya haddasa zubar da jini.
Haka zalika har yanzu gawar ta na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori domin gudanar da binciken abun da ya haddasa kisan.
A cewar Shugaban Ƙungiyar Alhaji Isiaq Agbaje mutane 11 wanda suka ji raunuka suna Asibitin a Ijagbo.
A lokacin da yake kiran ayi gaggawar kulle Makarantar tare da maida ɗaliban zuwa wata Makarantar sakamakon rikicin, Musuman sunyi kira ga Gwamnatin Jaha data samar da wata hukuma da zata gano waɗanda suka yi kisan.
Ƙungiyar tayi kira ga ƴansanda da suyi bincike akan lamarin domin kama waɗanda suka yi laifin.