Rikicin Naira: Ka Tausayin ‘Yan Nijeriya – Soludo ga Buhari
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi la’akari da irin wahalhalun da talakawan Najeriya ke fuskanta a sakamakon sake fasalin kudin kasar da kuma gyara musu halin da suke ciki.
Gwamnan ya ce wahalhalun da ake fama da su a yanzu suna da yawa, ya kuma yi kira gare shi da ya yi biyayya ga hukuncin da kotun koli ta yanke, inda ta ce tsofaffi da sabbin takardun kudi su zama takardar doka a yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Samari Albarkatu Na Kawai Suke Hari,Cewar Budurwa Mai Diri Da Ta Kasa Samun Saurayi Na Gaskiya
Soludo, wanda ya yi jawabi a yayin bikin jana’izar ministan sufurin jiragen sama na jamhuriya ta farko, Cif Mbazulike Amechi, ya bayyana cewa: “Ina mika godiya ga shugaban kasa kuma kwamanda a tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ministan sufurin jiragen sama ya wakilta cif Chris Ngige.
“Ina kira ga shugaban kasa da ya yi la’akari da irin radadin da al’ummar Najeriya ke fuskanta sakamakon sabuwar manufar sake fasalin Naira.
“Tunda Kotun Koli ta bayyana cewa tsohon da sabbin takardun Naira su ci gaba da zama a kan doka har sai an yanke hukunci, ya kamata shugaban kasa ya bi hukuncin da kotun koli ta yanke, wanda ya dora shi a matsayin Shugaban Najeriya.
A wani labarin kuma: Yakamata Messi Ya Yi Murabus Daga Buga wa Argentina Wasanni — Tsohon Kocin Real Madrid
Tsohon kocin Real Madrid Bernd Schuster ya bukaci dan wasan gaban Paris Saint-Germain Lionel Messi da ya yi murabus daga fafatawa Argentina wasannin kasa da kasa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Schuster da yake zantawa da kafar yada labarai ta MARCA ya ce, ” Messi ka iya ci gaba da wasan har nan da wasu shekaru, amma ya kamata ya kamata yayi murabus daga yi wa Argentina wasa.