Wata kyakkyawar budurwa mai diri ta koka kan yadda ta kasa samun saurayin da zai so ta tsakani da Allah.
Budurwar ta koka kan yadda duk wani namijin da zai so yayi tarayya da ita, kawai so yake ya amfana da baiwar da Allah yayi mata ta diri ya ƙara gaba. Rahoton jaridar Legit.ng
KU KARANTA KUMA: Ba Beli: Kotu ta umurci a cigaba da tsare Murja Kunya a gidan gyaran hali
Ta bayyana cewa mata irin ta masu diri da mazauna da kyawawa suna shan baƙar wahala a wajen samun so na gaskiya.
Budurwar tayi nuni da wasu irin ƙalubalen da take fuskanta ta hanyar yin wasu rubututtuka, ɗaukar kan ta bidiyo da hotuna waɗanda suka tabbatar da cewa lallai tana da diri.
A kalamanta:
“Da matuƙar wahala na samu so na gaskiya saboda maza yanayin halitttar jikina suke kwaɗayi. Mu ma mutane ne. Mun cancanci mu samu so na gaskiya.
“Samari na shakkun soyayya da mu saboda suna jin cewa kyawunmu ya wuce ace saurayi ɗaya kawai gare mu.”
“Wasu ƴanmatan basa son mu saboda suna jin cewa Allah yayi mana komai kuma rayuwar mu ta samu komai.”
“Ba namijin da kawai zai yi ƙawance da mu sai ya nemi ya ɗan amfana da albarkatun jikin mu. Rayuwa bata zuwa da sauƙi ga ƴanmata masu diri. Muna shan wahala sosai.
https://www.instagram.com/reel/CoiPjcsvsMa/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuraɗiyya ta tattaro:
@og_nelly1 ya rubuta: ”
“Maza suma suna fuskantar irin hakan. Abun har ya kai budurwa ta kalle ka ta ce maka ba zata iya soyayya da kai ba saboda ka cika kyau. Ni rayuwar nam wani lokacin sai in ji duk ta ishe ni.”
@barbie_mich ta rubuta:
“Ƴanmata masu diri da kyawawa sun fi shan wahala wajen samun saurayin da ba wasa ya zo ba. Idan kayi wasa kafin samun so na gaskiya duk sun gama tatse maka albarkatun jiki.”
Ana Dab Da Ɗaura Musu Aure, Matashi Ya Ritsa Budurwarsa Na Cin Amanarsa a Otal
A wani labarin na daban kuma, wani matashi ya ritsa budurwar sa na cin amanar sa a otal ana dab da a ɗaura musu aure
Wani bidiyo da aka sanya a manhajar TikTok ya nuna lokacin da wani ɗan Najeriya, ya yiwa matar da zai auri gwaji, inda ya gano cewa ashe ƴar hannu ce.