Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da sanarwar sakamakon bijirewa umarnin kotu a kan wanda ake kara, Shehu Wada Sagagi, kan bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na Kano.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta ruwaito cewa kwamitin riko na jam’iyyar PDP reshen jihar Kano, a ranar Asabar din da ta gabata, ya zargi tsohon shugaban rusassun shugabannin jihar, Shehu Sagagi, da kin bin umarnin kotu inda ya bayyana kansa a matsayin shugaban rikon.
Sakataren kwamitin riko na jam’iyyar PDP, Bala Aliyu ne ya bayyana hakan a Kano, yayin da yake zantawa da manema labarai abubuwan da ke faruwa a jam’iyyar PDP na Kano, inda ya jaddada cewa babu wani bangare a jam’iyyar.
KU KARANTA KUMA Rikicin Jam’iyyar PDP A Kano Na Neman Daukar Sabon Salo
Ya ce kwamitin ya shigar da kara ga ‘yan sanda da ma’aikatan gwamnatin jihar kan zargin aikata laifin da Sagagi ya aikata, wanda ka iya haifar da rashin zaman lafiya a jihar Kano.
A baya dai PDP ta gurfanar da Shehu Wada Sagagi, Bashir Tanko Mohammed, Ali Tijjani Ansaru Gambo, Jamil Abba zuwa kotu, inda aka yanke hukunci jagorancin akan mai neman karar na PDP.
Don haka a karar da ta shigar: PDP a matsayin wanda ake bin sawun shari’a da Shehu Wada Sagagai, wanda ake kara/mai kara, babbar kotun tarayya a ranar 9 ga watan Janairun 2023 ta yi gargadin cewa Sagagi ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar, don haka zai kasance da laifin raina kotu kuma za a kai shi kurkuku.
Sanarwar ta ce: ”Ku lura cewa sai dai idan kun bi umarnin da ke kunshe cikin wannan umarni na Kotun Daukaka Kara, don sanin:” Saboda haka hukuncin kotun da ke akai kara mai lamba FHC/ABJ/CS/393/2022 da aka gabatar a ranar 25/05/2022 ta Taiwo O. Taiwo .J ta ware kuma an soke karar FHC/ABJ/CS/393/2022 da aka shigar a ranar 25/032022.”
A Wani Labarin Kuma UNICEF Ta Horar Da Ma’aikatan Kiwon Lafiya a Fannin Hidima Ga Jama’a A Jihar Adamawa
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ya kammala shirye-shiryen horar da ma’aikatan lafiya kan samar da ingantattun ayyuka don magance matsalar karancin abinci mai gina jiki a jihar Adamawa.
Wakiliyar UNICEF a kasar Christian Munduate, ta shaida wa manema labarai jim kadan bayan ta duba cibiyar kiwon lafiya a matakin farko na Yelwa a Yola, babban birnin jihar a ranar Litinin.