Rikicin PDP: Ba za mu bada ƙuri’un mu ga wanda suka tsani Jihar Ribas ba – Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya sha alwashin cewa al’ummar jihar ba za su kaɗa kuri’unsu ga ƴan siyasar da ba su da alaka da jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwastam ta ƙaryata Gwanjon motoci sama da 7000 data ƙwace
Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a yayin kaddamar da tashar jirgin ruwa ta Orochiri-Worukwo.
A cewar Wike, al’ummar jihar Ribas a shirye suke su bijirewa maƙiya jihar ta hanyar kuri’unsu a 2023, yana mai jaddada cewa dole ne su ci gajiyar duk wani Ɗan Takara da zai samu kuri’unsu.
Ya ce, “Idan ka ce Jihar Ribas ba ta da matsala, Jihar Ribas za ta ce maka ba ka da komai a lokacin da ya dace. Idan ba ku son mu, ba za mu so ku ba. Idan kuna son mu, za mu so ku.
“Babu wanda zai yi amfani da kuri’unmu a banza. Kuri’ar mu za ta yi tasiri kuma jihar Ribas ta ci gajiyar duk wanda za mu mara wa baya.
“Siyasa a yanzu ba zabar wani ba ce, abin da za ku yi wa mutanen jihar Ribas ne.”
DAILY POST ta rahoto cewa ikirari na Wike na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP a matakin kasa.
Wike da magoya bayansa da magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun shiga takun saƙa tun bayan zaɓen Gwamna Ifeanyi Okowa a matsayin Abokin Takarar Atiku.