Kwamitin nan mai mutane 14 da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike suka kafa, domin duba yiwuwar sulhu tsakanin ‘yan siyasar biyu, zai fara aikinsa a Abuja ranar Litinin.
Atiku da Mista Wike sun amince da kafa kwamitin ne a wani taro da suka yi a ranar Alhamis din da ta gabata a Abuja a gidan tsohon ministan yada labarai na kasa Jerry Gana.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a taron da suka yi a makon jiya, wanda shi ne karon farko da suka zauna tare tun bayan da Atiku ya yi watsi da Mista Wike tare da nada gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, shugabannin biyu suka amince da wani tsari na warware sabanin da ke tsakaninsu.
Sun kuma amince cewa kwamitin zai duba korafe-korafen Wike da jiga-jigan jam’iyyar a sansaninsa tare da bayar da shawarwari kan yadda Atiku da shugabannin PDP za su magance matsalolin.
Ganawar da shugabannin biyu suka yi a makon da ya gabata ta fuskanci rudani, biyo bayan kalaman batanci da ke ci gaba da fitowa daga Mista Wike bayan kammala tattaunawar.
Gwamnan ya kuma ci gaba da hulda da shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a bainar jama’a, lamarin da ya kara rura wutar rade-radin cewa ya yanke shawarar sauya sheka zuwa APC ko kuma ya yi wa dan takararta Bola Tinubu aiki a zaben shugaban kasa na badi.
Majiyarmu ta ce Mista Wike bai janye daga yunkurin sasantawa da Atiku ba, domin ya bayyana sunayen wakilai bakwai na sansanin sa a cikin kwamitin.