Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, kuma karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, SAN, ya zargi babbar jam’iyyar adawa ta PDP da hannun wajen kiranyen ya yi murabus daga mukaminsa.
Keyamo a wata sanarwa da ya fitar a daren a karshen mako, ya ce bai karya wata doka ba, a iya sanin da yake da shi na doka, wato dai ya kasance a matsayin karamin minista kuma kakakin kwamitin yakin neman zabe na jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa aikinsa na kakakin kwamitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023 ko kadan bai shafi aikinsa na minista ba, inda ya ce yana amfani da dukiyarsa wajen gudanar da ayyukansa na jam’iyyar.
Rikicin PDP: Kwamitin Mutum 14 da Atiku, Wike Suka Kafa Ya Zaɓi Ranar Fara Aiki
A cikin sanarwar mai taken “Kiran nayi murabus, alamar firgici ce ga ‘yan adawa”, Keyamo ya ce zai yi wa kasarsa hidima tare da yi wa jam’iyyarsa hidima don ganin nasarar su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: ”na lura da wata sanarwa da wata kungiyar farar hula (CSO) ta yi cewa akwai sabani tsakanin aikina na Kakakin Yakin Neman Zabe da kuma na Minista a Tarayyar Najeriya.
“Na farko, ba tare da ma’anar wulakanta su ba, wadannan mutane ne da ke da cikakken alaka da jam’iyyun adawa amma suna kama da CSOs.
Ba zan iya tunawa ko wata magana irin wannan daga wadannan mutane a duk lokacin PDP lokacin da Ministocin PDP suka tsunduma cikin ayyukan yakin neman zaben Shugaban kasa ba.
“Tun da na zama Minista, Ma’aikatar ba ta samar da Mota daya don amfanin kaina ba.
Na yi sadaukarwa ga al’umma da motoci na da kayana, Wannan a yanzu yana cikin tarihin wajen aikina, kuma Babban Sakatare na na iya tabbatar da hakan.
“Saboda haka abin da ake kira matsayin wadannan mutane ba su da tabbas, ba su da masaniya kuma saboda haka an yi watsi da su.
Suna jin haushin kariyar da jam’iyyarmu da gwamnatinmu muke yi da kuma hasashen nasara ga Asiwaju BOLA Ahmed Tinubu (Dan takararmu) da muke yi.
”kuyi hakuri da wannan mataki nawa, amma dai zan ci gaba da hidimtawa Ƙasata, da kuma jam’iyya ta wato APC,” inji Keyamo.